Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Kyal Kyal Banza текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Best Of M Shareef Vol. 1


Nafison kyalkyal banza don na more rayuwa
Bana ji ban gani, ka barni nasha ruwa

Karki dau kyalkyal banza bai dai-dai ba a rayuwa
Aure yaki yanmata zan zamo miki garkuwa

Lokaci guda nafara jin kaunar ki
Natsuwa na rasa sa'ilin dana gan ki
Zuciya tana fadin kawai auren ki
Garkuwa in zama shugaba a wurin ki
Muyi auren sunnah ni da ke
Alkawar ni zana kula dake, yanmata, yar gata
Kazo kawai muyo soyayyah
Mu more rayuwa musha miya
A raina aure sam ba niyya
Da kyalkyali nake son duniya
Idan kana da sabon labari
Ka bani inji domin wannan bashi da guri
Karki dau kyalkyal banza bai dai-dai ba a rayuwa
Aure yaki yanmata zan zamo miki garkuwa
Nafison kyalkyal banza don na more rayuwa
Bana ji ban gani, ka barni nasha ruwa

Kinji dai kudurina gare ki alkhairi ne
Kar ki maida hannun agogo baya illa ne
Kar ki bar haske ki shige duhu sharri ne
Zuciyata ke take bida
Na fada kuma zani jaddada
Zaki fi kyawo a cikin gida mata ta
Nafison rayuwa da kyalkyali
Ko ido yafi kyau da tozali
Yanmata ado ga dandali
Takura ba za'ayi mini ba
Abinda na so ba'a haneni ba
Ra'ayina ka barni za nayi rayuwata
Karki dau kyalkyal banza bai dai-dai ba a rayuwa
Aure yaki yanmata zan zamo miki garkuwa
Nafison kyalkyal banza don na more rayuwa
Bana ji ban gani, ka barni nasha ruwa
Ina kiran ki da murya daya-daya
Son ki nake da zuciya daya-daya
Ke na kusanta kina ta ja baya, baya
Mun bambanta ra'ayi daya, daaya
Je ka huta ke kar kasha wuya
Zo muje musha icee cream masoyi na
Karki dau kyalkyal banza bai dai-dai ba a rayuwa
Bana ji ban gani, ka barni nasha ruwa

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Bako

2017 · альбом

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель