Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Haduwar Mu текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Best Of M Shareef Vol. 1


Haduwar mu tasa farin ciki a raina
Yanzu ke kadai nake ra'ayi
Haduwar mu tasa farin ciki a raina
Yanzu kai kadai nake ra'ayi

Na tsaya dake a so jaruma
Ke nake shirin yi wa hidima
Kyan ki kesa jiki yake tsuma
Ke na zaba abokiyar zama
Hankali yana kan ki na gano alama
Shi kadai ya isa nayi fahari

A tambaye ni wa na tsayar gwani
Amsar sa kaine ba yau ba tuntuni
Ni taka ce na baka izni
Saka ni ran ka ko'ina kaje dani
Zan taho ba jinkiri sanda ka kira ni
Tunda dai kana da kyan nazari
Haduwar mu tasa farin ciki a raina
Yanzu ke kadai nake ra'ayi

Haduwar mu tasa farin ciki a raina
Yanzu kai kadai nake ra'ayi
Ayo rubutu, sai mai karatu
Cikin batu, in nayi kure ki gyara
Lallai na fahimtu, kuma na iliman tu
Dadin batu ya sani bude hakora
Ilimi ake dashi bai barin babatu
Ni da ke mu dinga yin hakuri

Ina bayani, muna kamanni
Da kai da ni mun zamo daya
Na warke rauni, kin karrama ni
A sansani ke zan gano ke daya
Dan Adam a rayuwa na da rauni
Don haka mu dinga yin uzuri
Haduwar mu tasa farin ciki a raina
Yanzu ke kadai nake ra'ayi
Haduwar mu tasa farin ciki a raina
Yanzu kai kadai nake ra'ayi

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Bako

2017 · альбом

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель