Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya Ciki na samo ki nayi nasara a so ba damuwa Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya Ciki na samo ka nayi nasara a so ba damuwa ♪ Ba zan so ba, koda wasa bazan barki ba Na duba, a ciki ni banga kamar ki ba Mun saba, ni dake ba za'a raba mu ba Mun caba, in mu kayi aure munyo gaba Shine dai-dai, tun da ganin mu bar yin fargaba Ke na so tunda ni kika so hakan ne kyautuwa ♪ Kaine farko, kai na cira cikin su mazan gari Mai karko, wanda bai sa ni inyo jiri Muyi baiko, ni da kai ni tun tun tuni nayi shiri Da ka aiko, iyaye suyi ayiri-yiri A cikin auren nayi shiri na daukan hakuri Na yarda da kai zan zauna iyakar rayuwa Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya Ciki na samo ki nayi nasara a so ba damuwa ♪ Lallai, kauna ce da so Kin nuna gare ni Ko anki ni so Kece mai kula ni Nayi dace a so Abokai na kuji ni Ke nafi so a so In an tambaye ni Bana kallon ko wacce ya a cikin yanayi na so In bake ba banda abokiyar yin rayuwa ♪ So na dandana Zaki ya rufe ni In na rusuna Masoyi na daga ni Ni zan adana Sirri in ka bani Naki in bayyana Ko an takura ni Sam ba kowa idanu ba wanda suke gani Kaine dai wanda tun asali mukayo shakuwa Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya Ciki na samo ki nayi nasara a so ba damuwa Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya Ciki na samo ka nayi nasara a so ba damuwa