Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Azima текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Best Of M Shareef Vol. 1


Azima ke nake wa so na hakika
In ba ke ba babu wacce zan ba kauna ta
Ni Azima kai nake wa so na hakika
In ba kai ba babu wanda zan ba kauna ta

Zuciyata ke take muradi
Ke kike sawa inyo nishadi
Dan matso nan kusa muyi tadi
Babu wai-wai a so ana jihadi
Kisa atamfa zani saka yadi
Muyi fes-fes mu zagaya a gan mu a nuna
Kai na hango na taho gare ka
Da furen so shi nazo in baka
Tunda kasan bani da kamar ka
Jinjina ta nayi a gaban ka
Nayi biyayya ban bari ka koka
Tunda Aljannah ta tana kafar ka mijina
Azima ke nake wa so na hakika
In ba ke ba babu wacce zan ba kauna ta
Ni Azima kai nake wa so na hakika
In ba kai ba babu wanda zan ba kauna ta
Zo Azima masoyin ki na kira
Ki bani dama to ba nayi miki hantara
Na samu girma sanyi a rai na kankara
Tunda ni kike so haka nima sai ke
Ba nadama gamo dakai ka ankara
Zan yi tsama da makiyin ka ba jira
Karku soma ku ja da baya hattara
Tunda ni kake so haka nima sai kai
Azima ke nake wa so na hakika
In ba ke ba babu wacce zan ba kauna ta
Ni Azima kai nake wa so na hakika
An sani dani dake mun saba da juna
Bani yin sake kin zama 'yar lele na
Zan yi rayuwa dake har karshen rai na
Su gani da kansu kece zan nuna
Kyawun shigar ki ta zarce a raina
Ki fito su gan ki dawisu a guna iyyeh
Duk abinda zaka yi mini masoyi na
Baya sawa inji haushin ka cikin raina
Tunda na riga da na narku cikin kauna
Ni da kai kadai nake so in gana
In kaje dani hakika zan shana
Babu wanda zaya kalle ni ya raina iyyeh
Azima ke nake wa so na hakika
In ba ke ba babu wacce zan ba kauna ta
Ni Azima kai nake wa so na hakika
In ba kai ba babu wanda zan ba kauna ta

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Bako

2017 · альбом

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель