Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Wata Ruga текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Best Of M Shareef Vol. 1


Wata ruga, ruga, ruga
Wata ruga
Wata ruga na samo yarinyar Fulani
Ta shiga rai burin da nake muyi aure
Kai na sanar a soyayyah zo jani-jani
Wata ruga zan koma in nayi aure

Soyayyah ce, soyayyah ce
Soyayyah ta gare ki mai riba ce
Nayo nazari kinyi min tantance
Halin mu yazo daya haka riba ce
Ni na shirya ni zan sa kiyi dariya
Kema ki saka ni in zamo mai cin moriya
Nayi rawar gani cikin soyayyah
Tunda dake a yau na tako hanya
Mun chaba mu ake kallo bai daya
Ga yar fillo gani dan Hausa guri daya
Soyayyah taka ce tasa raina yayi fari
Na kai matsayin da babu mai ce mani in bari
In bakai ba miya ina ce maka gishiri
Mai yin kushen ka ni dashi ba sauran shiri
Ai sai muran ga wanda ya cika buri
Kyautar Allah babu mai maka gori
Da girman kogi naga bai kin kari
Na rike mulki dole inyi kirari

Bani canzawa a sonki ni ke na tsaya
Zo taho nawa Fulani ya mai kunya
Kinyi burgewa da shigar ki sam babu haya
Kin rike al'adar ki
Shi ya kara mini son ki
Wataran zamu wuce mataki
Randa zan zo in biya sadaki
Ki zam iyali na
A kai ki daki na
Ki bani hakki na
Da naki a guna
In zana je gona
Kiyi rakiya guna
Tunda kayi mani mai zai sa baza nayi ba
Inda soyayyah ba abinda ba za'ayi ba
Zanyi ma damu koda yaushe ba zan gaji ba
Inda rai nasan da rabon mu ba zaya ki ba
Kyan hali ne jarin ka dan Hausa
Tarbiyya na nan a gidan Hausa
Ka iya kalamai naji tattausa
Ayi auren mu ni fillo na kosa
Wata ruga na samo yarinyar Fulani
Ta shiga rai burin da nake muyi aure
Kai na sanar a soyayyah zo jani-jani
Wata ruga zan koma in nayi aure

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Bako

2017 · альбом

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель