Ruwan dare mai gama duniya Kaunar ki ce ta shiga ko'ina a jiki na Ruwan dare mai gama duniya Kaunar ka ce ta shiga ko'ina a jiki na ♪ Ruwan dare, kin zama a jiki na Kin zagaye ni kin shiga ko'ina Ina tunanin, dare ko da rana Na son ki ya zama jini na jiki na Ko nayi barci na kulle ido na Sai nai mafarki kin zo min guri na ♪ Muna a tare mafarki ya nuna Ko da ina nan ko baka gani na Hakan na dauka na sanya a raina Safe maraice kana zuciya na Ko nayi kuka kai ke share ido na In nayi tsokana na zo gun ka na tsira ♪ Na sanya jari inda ba a asara Na samu riba dole karfi na kara In dai a so ne na riga nayi zarra Allah ya bani tunda bani da dabara Sai godiya, kullum ni na kara Samun ki ya wuce a yi min harara Ruwan dare mai gama duniya Kaunar ka ce ta shiga ko'ina a jiki na ♪ Ruwan dare mai gama duniya Kaunar ki ce ta shiga ko'ina a jiki na Duk wanda yayi nema gurin rabbi ya dace Wanda yayi sabani akan haka ya kauce An ma jarabta ka dauke ta baiwa ce Samu rashi na rabbi ne karda kun mance Dauka ka sa a ran ka ni ta ka ce In mun yi aure na zarce wa tsara ♪ Hannu rike, a so dake mu kayi maja A bani ke, zama dake ina da hujja Muna rike tsayin dake babu keja Na sha rake na shantake na zama ninja Iya wuya, mun ki mu farrake, dangi ku zo ranar biki kuyi kara Ruwan dare mai gama duniya Kaunar ka ce ta shiga ko'ina a jiki na