Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Mariya текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Best Of M Shareef Vol. 1


Mariya
Ni na fidda waccha nake so a zuciya
Idan zan fada maku sunan ta, "Mariya"
Soyayya ciki nai dace a gaskiya
Na samu zabin Allah bani shan wuya

Masoyin ki nine fari
In same ki na cika buri
Ki ce "Nine bani in kare"
Zuwa gunki nai da alkahiri
Na kawo kalaman soyayya ki jiya
Domin ki ji dadi ke murna Mariya

Farinciki kai ne mai baiwa Mariya
Bakinciki in nai ka saka ni dariya
Da na gane ka sai inji na zam sarauniya
Aure na da kai nasan bani shan wuya
Ka duba cikin kauyen nan gaba daya
Ba wacce ta dace masoyi ya Mariya

Idan babu ke nima ba a gan ni ba
Duk idan kike nan gurin a min marhaba
Duk mai son ki ni ya so, ko ba haka ba?
Amman ba da soyayya fa ban yarda ba
Komai zanyi kan sanki banga aibu ba
Suna na ku chanja ku kiran' da Mariya
Soyayya ciki nai dace a gaskiya
Na samu zabin Allah bani shan wuya

Ni na fidda waccha nake so a zuciya
Idan zan fada maku sunan ta, "Mariya"
Na na rike alkawarin ka cikin rai na aje
Nake yin tsaro kullum ina tsaye
Bacin ranka bata so shi nake aye
Ai tunda kaima baka so nai hawaye
Duk inda ka sanya kafafu ina biye
Koda baka nan kana nan a zuciya

Na kulle ido na
A kan so da kauna
Kubar ma kira na
Mari' ita kadai na gani, na gani
Da kai zana zauna
In morai ma rai na
In san so da kauna
Sun aiki a jiki da jini, da jini
Duk inda naje dake zanyi tutuyi
Ko da zanyi labari sai na Mariya

Mariya
Ni na fidda waccha nake so a zuciya
Idan zan fada maku sunan ta, "Mariya"
Soyayya ciki nai dace a gaskiya
Na samu zabin Allah bani shan wuya

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Bako

2017 · альбом

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель