Nazari mudinga nazari Nazari mudinga nazari ♪ Kafin farawa gareku sai nayi sallama Abokai da yan uwa ga hanuna ku kama Nine naku M Sheriff dan karamin alarama Jariri a cikinsu mawaka ne wata rana a sama Ni nazo da yar nasiha ta gun al'umma Idan an maka shari dan uwa karda ka rama Wanda yasha madaci yau gobe kaganshi da zuma Mai gona ta shari shine zai girbi nadama-aa-aa-ah
Nazari Mu dinga nazari Nazari nazari Nazari In kaji anayin zancenka kai ka kai ayo ne In kadau wachan masoyi wani makiyi ne Ka wuce anata zagi wasu kuma yabo ne Ni dan nagane sai na toshe kunne Kaima ka toshe kunne bar hangen wane-wane Abinda Allah yaso kasamu wajibi ne Komai a hankali ne rayuwarmu tana a zane Rabon ka bai wuce ka koda kana a zaune Kukan kurciya jawabi ne inji mutane Ni koh inda zanyi nawa a baituka ne Karka fida rai da samu in kana araye Karka fida rai da samu in kana araye
Nazari Mu dinga nazari Nazari nazari Nazari Duniya duniya ce makaranta harda malami Dauki takandaka ka karanta da alkalami Karda ka yarda ayi maka rata dinga azumi Karka biyewa zuciya ta saka ka zauce Nemi tsari ga rabbi shedan kanka kar ya dace Addu'a ga mumini tazama garkuwa ce Allah sa mudace Zunubai mu kauce Toh sai mu jajirce ayyuka mu nace Nafi so ingani a sahun farko Nai yin murna da samun sakamako Kyakkyawa da an kira ni in miko Dacewa gun ihahu mui nema ba dan adam bah
Nazari Mu dinga nazari Nazari nazari Nazari ♪ Mu dinga nazari