Koko Koko Mai ganga doko haya ♪ Bismillah Allah na kirawo da farko Duk abinda nake yi shiyake bani iko Shike kareni in andana mini tarko In yaso insamu na shayi ko na koko In na rero wakata ganga na doko Guna yan mata da samari shako Suyi rawa da kidana a sannu in tura sako Duniya labari kunji shafi da farko Wani ya saki mata wani an mishi baiko Wasu sun subda wasu dauka su wanko Wani ya kare wani zai fara da farko Duniya nagane tana ajewa ta dauko Musulunci shi yace mu karama bako Mata a gida koh su zauna kar su leko In kana nema Allah kadai zaka roko In yabaka ka gode mai kuma sai ya ninko Gaskiya ka riketa a ko ina kayi karko Dauki wanda kakeso in baiba ka sako Hausawa muke zauna yarabawa dunko Dankali a hako kwaiba ita sai tsinko Zabi wace kake je ka ai muku baiko Kwanciyar mai sanyi zafi koh ya narko Zana zabi tuwo da miya in za'a girko Shukar da mukayi wata rana za'a hako Rabbi samu mu dace lahirar mu ta hasko Kuskuren da mukayi yafe mana kar mu dauko Domin darajar manzon nan daka aiko Na kira shi da konko Mai rayuwar dan tsako Ya hallata ayi ko Matarka jeka dauko Kasakata a boko Islamiyya shine farko Sunnah ta ma'aiki muyai riko Tashi tashi kuzo muyi sanmako Bani raina sana'ar mai dako Addu'a ta zarce ruwan jiko Allah ka tsare mu ga mai fako Tafiyar kai yafi kayo rako Godiya Allah mai iko Shi yayai mini kafar dana tako Da hanuwa ganga na doko Shi nake yin roko Shi nake yin roko Shi nake yin roko