Ki na nesa da idaniya Ki na kusa da zuciya Kin yo nesa da idaniya ta Ki na kusa da zuciya ♪ Jigon rayuwa soyayya ce Na taba jin hakan sai na mance Da naga mai kuka asSo in ce kauce Iya tunani na mai haka ya zauce Yanzun gashi nan akan kai na, ina kuka kan Soyayya ♪ Mun yiyo sabo da ke muna tare Kullum in zo zance wurin ki in zanzare Shaƙuwa ta kai Shakuwa aboki in karkare Mun fara tunanin aure muja zare Rashin ki yasa rana ya zam dare Bana iya barci da idaniya ♪ Duniya tayi daci Rashin kine Bana iya barci Domin ki ne Na zam a kadaici Gani a jingine Rayuwa ta kunci Yayi kane-kane Yaushe hawaye zai bar zuba, kzo ki tare aminiya ♪ Yaya zan yi in misalta soyayya Yaya zan yi in fasalta soyayya Ita ce ba'a saye da kudi duk dukiya Ita cemai gida na mulki shine zuciya Ta sanya mai ƙarfi ya sunkuya Ya zubda hawayen idaniya ♪ Ki na nesa da idaniya Ki na kusa da zuciya