Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Bani Canzawa текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Ni Da Ke


Bani canza wa
Nima bani canzawa
Bani canzawa
Kai nake kauna
Bani canzawa ke nake kauna
Na fada na kara fada
Bani canzawa kai nake kauna
Na fada na kara fada

Zuciyata ke take muradi,
Nayi fata da ke mu dinga tadi
Zanyi koda zaki sa ni gadi
Kinyi karfi a zuci kinfi rodi
Ra'ayi riga, mai kida ganga zo buga abar so zanwa yabo

Hankali ya karkato gareka
Kunnuwa na sunfi so su jika
Murmusa min idanuwa su ganka
Zana zauna da kai ko a bukka
In na burge ka, saurayi tanka, zantuka dake bakinka zubo

Komai nayyo yan uwa kuyimin uzuri na
So ya janyo faruwa karku gano laifi na
Ni na sanyo taguwa ta sanki gata jikina
Ki oyoyo na kawo ga tsaraba hannu na
Kin shige raina, baki damu na, nayi sa'a
A so na samu rabo

Eh jininka shi da nawa sunkayo garwaya
Almakashi bai yanka so sai dai igiya
Da garwashi a ce inbarka ni na kiya
Ba fushi sai hakuri zaman duniya
Kai ka dai gayya
Dan fito ka tsaya
Kayi girma ka zarce dabo
Bani canzawa ke nake kauna
Na fada na kara fada
Bani canzawa kai nake kauna
Na fada na kara fada

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Bako

2017 · альбом

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель