Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Na Yarda Dake текст песни

Исполнитель: Umar M. Shareef

альбом: Farin Jini


Na yarda dakaine farin ciki na
Na yarda dake masoyiyata
Na yarda dakaine farin ciki na
Kin bani abin dana baki
Kin soni a sanda na soki
Kika bani kujerar mulki
Kika yi mini kautar doki
Samun ki nayi dabara
Barin ki zanyi asara
Na roki rabbi tabara
Da yabani ke zana jira
Ni kaka martaba
Baki guje ni ba
Bazan auri wanin ki ba
Ai tunda banga kamar ki bah
A soyayya
Baka bukatar in ma tini
Mai sonka nece kasani
Na gaishe ka ina wuni
Soyayyar ka na acikin jini
Da kai nasaba tun farko
Da kai na yarda a mini baiko
Farin cikina kai ne
In nayi kuka kai ne
Koh ban so ka ba
Bazan ki ka ba
Jani muje gaba
Don banga kamar ka ba
Kin rike amanata
Kin boyeta kinki nunata
Zancen rabuwa ku dainata
Koh mun saba zamu sasanta Tsakaninmu mu daidaita
Jini da jijiya
Komai dadi wuya
Mun dauki alkawari
Zamuyi zaman hakuri
Kince bayani nace bayake
Kin kula dani zan kula dake
Masoyina gangariya
Tauraron duniya
Soyayya ka iya
Agurinka a kwaikwaiya
Kai ke koran haushi da gaka ina a cikin halin damuwa
Kanai mini rarashi kasa naji babu yani cikin duniya
Rabin jikina kai ne
Idon gani na kai ne
Sanyin zuciya
Kasani nazam sarauniya
A soyayya
Na yarda dakaine farin ciki na
Na yarda dake masoyiyata
Na yarda dakaine farin ciki na

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Bako

2017 · альбом

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель