Shikenan Shikenan Shikenan soyayya ta kulu Shikenan soyayya na kamu Shikenan soyayya ta kulu Shikenan soyayya na kamu Cuta ta so kin mini magani Na baki so kinki ki bada dani Ke dai a so idanu ke gani In kika daina so nima kin tsai dani In kina so ina so muna so Baka so ba so shikenan Kai ne gwani a guna ba ya kai Mai ji dani me zan yo babu kai Kasan dani ina da tsansar ji da kai Ka zama magani in da kai to zana kai In kana nan ina nan muna nan In baka nan bana nan ba muwa nan Shikenan Ni koda babu kowa zan zauna dake Ruwa ko da tsawa ina nan dake Ko kazama gawa a raina kake Tarkon magauta sai mun tsallake Bacin ranki bacin rai baki cikina Dariyarka dariya farin cikina Shikenan soyayya ta kule Shikenan soyayya na kamu Ni zan tafi raka ni muje waje Ke kinka fi a gidana in aje Ki sharafi hajarki ki barbaje Ga tallafi in zaki kasar waje In kina chan ina chan muna chan In baka chan bana chan zan tsaya nan Na zama daliba Kaine malami Kai zan martaba in samo ilimi Gun 'ya'yana uba Bani da zulumi Zoka wuce gaba na riga na salami Ina kin wanda ke kinka masoyi Ina son wanda ke sonka mijina Shikenan soyayya ta kulu Shikenan soyayya na kamu Shikenan Shikenan.