Kyakwawar fuska na kalla ta deben kewa Kuyi min san barka na samo fitilar 'yan mata Kyakwawar fuska na kalla ta deben kewa Kuyi min san barka na samo dan auta na maza ♪ Masoyiya, masoyi na kai ne Aminiya, aboki na kai ne Ke zuciya, rabin raina kai ne Ke jijiya, jinin jikina Kin zama komai na, abun kallo madubi na Kai ne tinanina a barci na da mafarki na Ban bari ki cutu Zan zama garkuwa Komai yake zuwa Gareki zana tare shi ♪ Adadi na ruwan sama wanda suke zuba Adadin kifaye ma ba a san su ba Adadin bishiyoyi baza su kirgu ba Haka soyayyarki a rai ban santa ba Koda za'a au'na ba sikele wanda zai dauka Bata misaltuwa soyayya wace nake miki a zuciyata An san farkon rikici, ba a san karshen sa ba Soyayya gamu ciki, baku san haduwar mu ba Alkhairi ne a ciki, sam sam ba sharri ba Karda ku ce, "Zaku raba, bazaka ku iya ba" ♪ Zan fesa turare Inzo in zauna in bude hakore In ta murna, Allah sarki zare Dukanin fargaba Angoye amare Mu a nuna ni dake a tare Zamu zauna rayuwa ta kare A tare har abada Kawaye ku kalla Shi na ba akalla Wanda bai so nai kwalla Nima bana so yayi Ke na tsayar zabi na Na sanar dangina Zana turo abba sa rana ayi Wajibi in kwantar da kai Munyi aure ni da kai Karshen biyayata ga kai Zanyi tunda ina ji da kai Kyakwawar fuska na kalla ta deben kewa Kuyi min san barka na samu fitilar 'yan mata