Kishore Kumar Hits

Ali Jita - Rukayya текст песни

Исполнитель: Ali Jita

альбом: Rukayya


Sannu sarauniya Rukayya
Wanka gunki zasu koya
Gimbiya yar dagwas Rukayya, dan Allah gabansu juya
Kinzama garkuwa Rukayya
Kiyi magana ki tara gayya
Mai halin kwarai Rukayya
Kece mai dubun masoya
Tauraronki na dagawa
Mai haske kamar Surayyah
Menene gimbiya Rukayya?
Wake damun Rukayya?
Mai hakuri ina rukayya
Yar asali Ina Rukayya
Kyakyawa gimbiya Rukayya
Wanka sai wajen Rukayya
Akwai tsafta wajen Rukayya
Ina buga tambaran Rukayya
Mata nata tambaya
Giwa za a bata girma lallai babu magiya
Ai inkaji wance wance ce, domin tai gwagwarmaya
A duba Rukayya gimbiya
Tun yarinta da tarbiya
'Yar manya 'yar sarakuna, kune ke haska duniya
Dubu tasha gaban dari, dagani ai babu tambaya
Kura kuma bata cin kashin gwiwa sai dai ta gwagaya
Ga dan kolo da malami, sai an raya tsangaya
Yara kunga Rukayya jaruma, nidai nabada inkiya
Sannu Rukayya sannu-sannu kowa ke yawa maraba
Sai nasara da dadadawa, sam bakisan bakin ciki ba
Allah neh yake tsareki, ba boka da dan Adam bah
Yanzu yabo muke agunki, ba kago halin muke ba
Muyi jita musa sarewa, bazai chanzan salan kidan bah
Yan yara nata har-harakawa, manya ma ba'a hana ba
Mun tina toshiya ta dauri, bazance kara bace ba
Linzamin ya girma kaza, koh akuya bata nada bah
Sama dai ta darar ma yara, sai hange basa taba ba
Yanzu Rukayya ce a fili, tauraronta bai dishe ba
Kainuwa dashin Allah, yanzu Rukayya tafi karfin su
Mai gado na zinari kece zaki gaji Balkisu
Kiyi ado na alkeba mata na kiranki dawisu
Wacce duk ta zageki lallai zata dinga nida su
Rukayya ai sarauta ce mata sun fada da bakinsu
Masu so suje bude ido nan zasu kara kallonsu
Masu so abasu abasu nan zasu mika hannun su
Sannu dai Rukayya, Rukayyatu gimbiya ta mata
Sannu dai Rukayya, Rukayya jaruma ta matan duniya

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель