Kishore Kumar Hits

Ali Jita - Tambura текст песни

Исполнитель: Ali Jita

альбом: Tambura


Prince production
Ga tamburan masoya
Ga baitukan masoya
Ku fito rawa masoya
Ba yara babu manya
Shi so ya tara gayya
Kuma so ya watsa gayya
Soyayya ruwan zuma ce in ka sha ka ba masoyi
Soyayya farar zuma ce waccha a yau ake ta yayi
Soyayya farin ciki ce mai yaye bakin ciki ce
Indai da so da kauna ayi komai daren dadewa
Ita duniyar masoyiya ai filin ta bai matsewa
Komai duniya tabawa, soyayya ana dadewa
Sakon zuciya da lura an aika yana isarwa
Ku tambayi zuciyar masoya
Ta sarka da bai katsewa
Ga tamburan masoya
Mai jita yana bugawa
Soyayya ruwan zuma ce
In ka sha ka ba masoyi

عسسلم سالم, عليكم, magana ta da sallama ce
A ciki salo na waka, kuma in sanya dan kwatance
Ni na san hali na kauna soyayya ruwan zuma ce
Wasu sun sani da baki wasu a karance ko rubuce
Su dai tambura na jita ba kashe kunnuwa sukeyi ba
Ga tamburan masoya
Mai jita yana bugawa
Ga sako wurin masoya
Kuyi hakuri wajen rikon ta
Kar da ku damu dan magwata dan wasu masu shirya keta
A kulla rikon amana, tabaraka jalla ya rubuta
Ina mafita gurin masoya? Zaku ji ga Ali jita
Soyayya tana da dadi
Ba karya nake fadi ba
Ga tamburan masoya
Mai jita yana bugawa
Ruwa, iska gami da sanyi
Alkawari bazai gusa ba
Wani zai so ka ne da rana
Da daddarai bai ki ka mace ba
Wani zai so ka dan amana
Ko bai baka ko kobo ba
Idan Allah yai ma masoya ba kai kuka a duniya ba
Bude idon ka dubi nawa
Bazan sakaci da addu'a ba
Ga tamburan masoya
Mai jita yana bugawa
Mai san ruwa a gora shi ne zaya rabi tulu
Chillan cikin mazaje wannan an kira ta delu
Soyayya tana da tsari
Bata rarrabai kabilu
Na saka Hausa nai' misali
Idan magana kawai ta kullu
Idan hausa ne azanci ba gaza magana nake ba
Ga tamburan masoya
Mai jita yana bugawa
Ya Allah ka kauda sharri
Sharrin aljanni mutane
Da yan hasada da kyeta sun gaza zaune ko tsugunnai
Toh tunda jalla yayi, yaya zasuyi da rai ne?
Kuyi hakuri kawai ku barmu
Komai kunga kaddara ne
Sunyi kadan su chanja wannan, basa chanja kaddara ba
Ga tamburan masoya
Mai jita yana bugawa
Soyayya ruwan zuma ce
In ka sha ka ba masoyi

It's Prince on the beat

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель