Kishore Kumar Hits

Ali Jita - Gari Ya Waye текст песни

Исполнитель: Ali Jita

альбом: Gari Ya Waye


Tantabara da tara kwai tara
Zani gari tara inga mutum tara
Prince production
Allah yayi dare gari ya waye
Shi mai sanka bayama tawaye
Gwara ku daina hantarar dan gaye
Masu gada da dan kara ta lauye
Ali Jita ke zance
Maganace da kwatance
A ciki insaka zaurance
Hikimata nasarace
Wanda ya sanni ya rigaa ya gane
Soyayya kamar kace tsuntsune
Alheri kunga mai naso ne
Shi sharri ku gane dan aikene
Wanda yasoka ya riga ya soka
Makiyinka ya riga ya kika
Yabar ta tashi yayi ta taka
Allahune yake fissheka
Na yarda duniya labari
Mai kiwon kare yana shan haushi
Mai tantabara yana gani an tashi
Mai kyashi aradu sai buzunshi
To nine nake misalai
Rigace daba maballai
Wanda ya waiwaya a kallai
Ninasan akwai dalilai
Wanda ya waiwaya anan an barshi
Dana kwarai a zuci shike kishi
Tafiya babu waiwaye sai mashi
Ango shiyasan dalilin toshi
Magana ba shikeba
Kuma bazan kasaba
Ban iya zalinchi ba
Ban koyi halin wanchanba
Wanda ya sanni ya riga ya sanni
Na rike gaskiya ta zamto tsani
Ba sanadin da wanni zai zageni
Harda kudi ake biya dan a ganni
Wani baisan bashi ba
Be iya ya maida ba
Baisan da akwai illa ba
Yin haka bai dace ba
In an baka ya kamata ka maida
Mai kayan aro ina zai saida
Yan mata kuna da kyau munshaida
Koba foundation ace ba hoda
Ali Jita, Ali Jita, yara kuce Ali Jita
Mai jita, kada jita
Allah yayi dare gari ya waye
Allah yayi dare gari ya waye
Mai hakuri, kayi hakuri
Ba'asan gajan hakuri
Mai hakuri, dada hakuri
Akwai riba wajen hakuri
It's Prince on the mix

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель