Kishore Kumar Hits

Ado Gwanja - Naji Dadi текст песни

Исполнитель: Ado Gwanja

альбом: Naji Dadi


Kasheepun Kida
Naji dadi shine garin zama
Sai masoyi ke maka hidima
Ludayi ne tsagin jikin duma
Tabbaci ne ke kauda tantama
Naka dai shi ne naka karkaje nema
Kan kazam wane a duniya akwai fama
Tunda tarko sa'arsa na jikin burma
Mai shiga kogi zaiga martabar koma
Masu sanyi na jiki basayi bori ba

Mai shirin barci karkai badi ba nan ba
Bani son tauye hakkin wani ba nauba
Saki citta don bata yanayin kimba
Duniya mai tsumayin wanda baizo ba
Daina sauri rabonka bazaya wucema ba

Nasako kura masu tunkiya sun kama
Cikin dubu dai ba a cire biyar ko goma
Bana alfahari karku ce dani dan kama
Kar kuce min dutsen fashin tama
Bari dan dawayya uban duma
Ni nasan sabo da yan maza shine jari
Nida mata har gobe sai dai fatan alkhairi
Masu turmi daka
Ke da shikar daka
Tankade ma haka
'Yara'ye

Midget mix
Girgidi dai bazai rike tarkon turke ba
Banji zara ta kyale dami ya zauna ba
Masu tatsa basa jimirin dauko sanda
Masu sassaka bazasu ga kwancen gamji ba
Masu tirmi dai bazasu daka don kurbi ba
Haka kura bazata mace don nama ba
Dundumi dai koya rufe ido ba
Dariya dai baso bace bama nagane
Kama dai da wane bai nufin wane
Maida alkhairi gun zamansa daidaine
Bata kwana wutar kara fa nagane
Babu shakka nagane so ya tsuntsu ne
Sai ya taso kan wane yai tabin wane
Zanaci yazama dole in rabo nane
Banga ranar tayar da hankali na
Beat Amjad record

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Iye

2023 · сингл

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель