Kishore Kumar Hits

Ado Gwanja - Salma Amarya текст песни

Исполнитель: Ado Gwanja

альбом: Salma Amarya


Salma amarya mai halin wanke tukunya
Bar magauta suci baya gobe karya taci karya
Ko su ki koh su so (ko su so)
Ai Salma koh su ki koh su so (haye ko su so)
Musa ne angonki (Musa ne)
Ya Salma Musa ne angonki (Musa ne)
Kin kyale masu kunfar baki (gasu chan dai)
Yau zaki tai cikin dakinki (Musa ne fa)
Na gidanki gaki angonki
Dan Musa dai yana kishinki (eh mana)
Koh su so (haka) koh ma kar so (muna nan dai)
Koh subi koh ma kar subi (muna nan dai)
Lokaci sai mai lokaci (haka haba)
Koh suci koh ma kar suci (Muna nan dai)
Zamuje koh basa son muje (in Allah yaso)
Ga amarya ga ango (gani)
Haba Musa me kake jira Gagare (tashi tashi)
Daga yanzu kazamo jigo (wayo)
Tunda dai Salma amarya koh ina ta tare (ya kuke gani)
Auren yar Kano da dan Gombe (yayi yayi dai)
Duk yan hassada su rarabe (koh basu ji ba)
Mu koh ina Kano ina Gombe (a fada musu)
Ya Allah kasa mu kai gobe
Amarya Salma me kike nufi ne
Ga kawayenki gamun nan a zaune
Tashi jujuya mai kike jira ne (ya amarya)
Tunda nufin ubangiji ne
Ai bikin chan haka su na yaudara ne (ya amarya)
Shi komai fah kaddara ne
Zo mu zauna zo muyo fada ne (ya amarya)
Biki yakai biki su Kwashewa sun zo
Akwai Dankwairo na Tafa ma na nan yazo
Ibrahim Musa na Tafa dangin Dankwairo
Ibrahim Musa abar ka sai ta Allah tayi
Amanata bata karewa Musa
A kyale mu sai ta Allah Dan Musa
Dan Musa na Kwashewa (wayo)
Na dan Gwanja Dan Musa ka hutawa
Aikin dare sai su gwani ba rago ba
Ai mai duma bai hana shan kokiya
Gadon kudi ba gadon arziki ba
Don arziki baiyi kama da tsiya ba
Domin tsiya ai bata daura aure
Mata kuzo mu tsitsigar duniya da tsinke
Ita dai kyada kadan tai satar kama da wake
Domin gidana na Dan Musa babu wata sai ke (Salma)
Amarya Salma special (haka) kuma soshiyar
Tana bin sabgarta manual (totally)
Ai amarya bata da rigima
Kuma Salma, bata bin dangin masu hadama
Ke Salma, Salma bata da yawwan dakadama (da ganinta)
Shi ya sanya bata da rigima
Haye Salma daure Salma daure dai
Musa daure Musa daure dai

Hayya, amarya Allah gidanku komai sun miki
Ya amarya gidanku komai sun miki
Kina nan dai gashi zaki tai chan dakinki
Babu wasu masu hanaki
Yau biki ga danginki
Naga dangi na mijinki
Ga abokai da kawaye sunyi zaune
Sunyi zaune amarya Salma

Поcмотреть все песни артиста

Другие альбомы исполнителя

Iye

2023 · сингл

Похожие исполнители

DJ Ab

Исполнитель